Zabura 29
1Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.
2Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.
3Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.
4Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.
5Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.
6Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.
7Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.
8Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.
9Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”
10Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
11Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath