Kiristanci
baya

Zabura 28

1A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.

2Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki.

3Kada ka ja ni tare da mugaye, tare da masu yin mugunta, masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu amma suna riƙe da su a zukatansu.

4Ka sāka musu da ayyukansu da kuma don mugun aikinsu; ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi ka kuma mayar musu abin da ya dace da su.

5Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba.

6Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai.

7Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

8Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa.

9Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath