Kiristanci
baya

Zabura 26

1Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.

2Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;

3gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

4Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;

5na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.

6Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

7ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.

8Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.

9Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai

10waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.

11Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.

12Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath