Kiristanci
baya

Zabura 24

1Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;

2gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.

3Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

4Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

5Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

6Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela

7Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.

8Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.

9Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.

10Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath