Kiristanci
baya

Zabura 1

1Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

4Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

5Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath