Kiristanci
baya

Zabura 148

1Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.

2Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

3Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

4Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

5Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

6Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

7Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

8walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

9ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

10namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

11sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,

12samari da ’yan mata, tsofaffi da yara.

13Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

14Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath