Kiristanci
baya

Zabura 146

1Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.

2Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

3Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.

4Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.

5Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

6Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

7Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,

8Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.

9Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.

10Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath