Zabura 143
1Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini.
2Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
3Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni.
4Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai.
5Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
6Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela
7Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
8Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina.
9Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.
10Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.
11Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.
12A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath