Zabura 130
1Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
2Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.
3In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
4Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.
5Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
6Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
7Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
8Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath