Kiristanci
baya

Zabura 12

1Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

2Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.

3Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,

4masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

5“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

6Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.

7Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

8Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath