Kiristanci
baya

Zabura 126

1Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

2Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

3Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.

4Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.

5Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

6Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath