Kiristanci
baya

Zabura 125

1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

2Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.

3Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta.

4Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

5Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath