Kiristanci
baya

Zabura 122

1Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

2Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

3An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

4A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.

6Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”

8Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

9Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath