Zabura 120
1Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.
3Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?
4Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
5Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!
6Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.
7Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath