Kiristanci
baya

Zabura 114

1Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,

2Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.

3Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;

4duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.

5Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,

6ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

7Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,

8wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath