Kiristanci
baya

Zabura 101

1Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.

2Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi

3Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba.

4Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

5Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

6Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

7Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

8Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath