Kiristanci
baya

Yoshuwa 23

1An daɗe bayan da Ubangiji ya ba Isra’ilawa hutu daga dukan abokan gāban da suke kewaye da su. Yoshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa,

2sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa,

3ku kanku kun ga dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi da idanunku wa dukan ƙasashen nan, Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.

4Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma.

5Ubangiji Allahnku kansa zai kore su a madadinku. Zai fafare su a gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu, yadda Ubangiji Allah ya yi muku alkawari.

6“Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba.

7Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu.

8Sai dai ku riƙe Ubangiji Allahnku da kyau, yadda kuka yi har zuwa yanzu.

9“Ubangiji ya kori manyan ƙasashe masu ƙarfi; har wa yau ba wanda ya iya cin ku da yaƙi.

10Mutum ɗaya a cikinku ya isa yă sa mutane dubu nasu su gudu, domin Ubangiji Allahnku yana yaƙi dominku, kamar yadda ya yi alkawari.

11Saboda haka sai ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.

12“Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su,

13ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.

14“Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.

15Kamar yadda Ubangiji Allahnku kuwa ya cika kowane alkawari mai kyau, haka ma ba zai fasa kawo muku bala’in da ya faɗi ba, sai ya hallaka ku daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba ku.

16In kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku wanda ya umarce ku, in kuka je kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka rusuna musu, fushin Ubangiji zai sauko a kanku, za ku kuwa hallaka da sauri daga ƙasan nan mai kyau da ya ba ku.”

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath