Kiristanci
baya

Ayuba 11

1Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,

2“Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne?

3Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?

4Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’

5Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba

6yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.

7“Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?

8Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?

9Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.

10“In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?

11Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?

12Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.

13“Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,

14in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba

15shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.

16Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.

17Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya.

18Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.

19Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.

20Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.”

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath