Kiristanci
baya

Hosiya 3

1Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”

2Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir.

3Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare da ke.”

4Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki.

5Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath