Kiristanci
baya

Ibraniyawa 3

1Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.

2Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.

3An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.

4Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.

5Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.

6Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.

7Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

8kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,

9inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.

10Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’

11Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

12Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.

13Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.

14Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.

15Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”

16Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba?

17Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba?

18Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?

19Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath