Kiristanci
baya

Ezekiyel 15

1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

2“Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi?

3An taɓa ɗaukan itacensa an yi wani abu mai amfani? Akan yi maratayi da ita da za a rataya wani abu a kai?

4Bayan kuma a jefa ta cikin wuta, wuta kuma ta cinye kowane gefe ta kuma babbaka tsakiyarta, tana da amfani don yin wani abu kuma?

5In ba ta da amfanin wani abu sa’ad da take cikakkiya, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?

6“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kamar yadda na ba da itacen kuringa a cikin itatuwan kurmi ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama.

7Zan yi gāba da su. Ko da yake sun fito daga wuta, wuta za tă cinye su. Kuma sa’ad da na yi gāba da su, za ku san cewa ni ne Ubangiji.

8Zan mai da ƙasar kufai domin sun yi rashin aminci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath