Amos 7
1Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa.
2Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
3Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
4Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa.
5Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
6Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
7Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.
8Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
9“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
10Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba.
11Gama ga abin da Amos yake cewa, “ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
12Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can.
13Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
14Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.
15Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
16Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
17“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath