Kiristanci
baya

1 Tessalonikawa 1

1Bulus, Sila da Timoti, Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi. Alheri da salama su kasance tare da ku.

2Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu.

3Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.

4Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku,

5domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.

6Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.

7Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.

8Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai,

9gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya,

10ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath