Kiristanci
baya

1 Korintiyawa 3

1’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai.

2Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.

3Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?

4Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

5Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa.

6Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma.

7Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma.

8Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa.

9Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini.

11Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.

12In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara,

13aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa.

14In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada.

15In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.

16Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?

17Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.

18Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima.

19Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu” ;

20kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”

21Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne,

22ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne,

23ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath