1 Tarihi 1
1Adamu, Set, Enosh,
2Kenan, Mahalalel, Yared,
3Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.
4’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet.
5’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.
6’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat da Togarma.
7’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
8’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.
9’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan
10Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.
11Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa,
12Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.
13Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa,
14Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa
15Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
16Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.
17’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek.
18Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.
19Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.
20Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera
21Hadoram, Uzal, Dikla,
22Ebal, Abimayel, Sheba,
23Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
24Shem, Arfakshad, Shela,
25Eber, Feleg, Reyu
26Serug, Nahor, Tera
27da Abram (wato, Ibrahim).
28’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.
29Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,
30Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema
31Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.
32’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.
33’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.
34Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila.
35’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora
36’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek.
37’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza.
38’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.
39’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.
40’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana.
41Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
42’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.
43Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.
44Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.
45Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.
46Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.
47Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.
48Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.
49Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.
50Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.
51Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet
52Oholibama, Ela, Finon
53Kenaz, Teman, Mibzar,
54Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.
tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
WEBREATH · 11:11
«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25
Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.
WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath