Kiristanci
baya

1 Tarihi 10

1To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.

2Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.

3Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.

4Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.

5Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.

6Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.

7Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.

8Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.

9Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.

10Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon.

11Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu,

12sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.

13Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba,

14bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.

tushe: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

WEBREATH · 11:11

«He himself gives everyone life and breath and everything else» — Acts 17:25

Breath is one for all: everyone lives by it, whoever they are and whatever they believe. Every day at 11:11 local time people stop for sixty seconds, breathe, and thank GOD for the breath — each in their own words, each within themselves. In that minute we are One Breath.

WEBREATH — the Minute at 11:11, your own local time — we are One Breath